Wata giwa tayi fada da zakuna guda 14
Wata matashiyar giwa ta samu damar kubuta daga wasu azzaluman zakuna harsu 14 bayan da sukayi yunkurin kashe ta.
Acewar rahoton, giwar dai ta samu damar kubutane a hannun wasu azzaluman macen zakanya kuda 14 inda ta wuce daga baya babu ko kwarzane daya a jikinta. Wannan al'amarin dai ya farune a kasar Zambiya.
Babu wanda dai baiyi tunanin cewar zakunan zasu kashe giwan nan wanda har zakuna guda uku sukai ta hawa bayan ta suna kokarin kada ita.
Zakuna tare da giwa alokacin da suke tsakiya fada.
Hotunan dai tare da kuma bidiyon sun suna kayitaccen fadan na dabbobin guda biyu. Giwar dai da aka taru mata tayi iya kokarinta inda ta kwaci kanta daga baya daga wajen zakuna bayan data wuce babu ko kwarzane a jikin ta.
Saboda haka, wannan darasi ne ga mutane da sauran abubuwan da suke saurin mika wuya ga abu ba tare da sun gwada kokarin su ba akan sa.
Asali: Legit.ng