Wani mutum ya dawo gida yaga katon kadangare

Wani mutum ya dawo gida yaga katon kadangare

Wannan babban halintar dai ta samu damar sulalewa ta shige bayin wankan wani mai daukar hoto. 

Wani mutum ya dawo gida yaga katon kadangare

Idan kasan iya yawan mahimmancin matsayin da  aikin daukar hoto yake dashi, to yana kuma da kyau kayi tunanin ta wani fannin game da hatsarin da aikin yake tattare dashi a fadin duniya, musamman wajen daukan abu mai ban tsoro hoto.

Anan wani mutum ne mai suna Mark MacEwen, ya dade yana daukan rayuwar irin wannan katon halittan na babban kadangare hoto kai harma yayi musu bidiyo a wasu lokutta. Wata rana bayan ya dawo daga aiki, sai ya shiga bayi domin yayi wanka, kawai saiya tarrad da katon kadangaren nan mai hatsarin gaske a cikin bayi. Ashe abun dake faruwa kenan idan mai daukan hoto yaga irin wannan abun sai ya yanke shawaran barin gidan?

Abun mamaki dai daga karshe, MacEwen, ya samu sa'ar samun wasu mutane a kusa dasu inda suka samu damar fitar da katon halittar daga cikin gidan nashi.

Gaskiya daga yau bazan kara zuwa bayin nan da kaina ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng