An kashe mutane 40 a wata mahakar zinari a jihar Zamfara

An kashe mutane 40 a wata mahakar zinari a jihar Zamfara

- Wasu yan bindiga sun kashe kimanin mutane arba'in a jihar zamfara

- Sun kai harin ne a wata mahakar Zinari dake kauyen Bindim na karamar hukumar Maru

- Ana zargin yan bindigan masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne

An kashe mutane 40 a wata mahakar zinari a jihar Zamfara
Yan bindiga sun kai hari a wata mahakar zinari dake jihar Zamfara sun kashe mutane 40

Rahotanni daga jihar Zamfara sun ce kusan mutane arba'in (40) ne aka kashe a cikin wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai kan wata mahakar Zinari.

KU KARANTA KUMA: Saraki ya magance rashin aiki, ya samar da ayyuka 40,000

Haka ma wasu mutane da dama sun bata yayin da wasu suka tsira da munanan raunukka a cikin harin da aka kai ranar Litinin kan mahakar zinarin wadda ke daura da kauyen Bindim na karamar hukumar Maru.

Mazauna yankin sun shaida cewa harin ya zo bayan da 'yan bindigar wadanda ake zaton 'yan fashin shanu ne suka kwashe makonni suna satar mutane don neman kudin fansa.

''Yawancin wadanda suka mutun lebarori ne masu aikin hakar zinari da kuma wadanda suka zo saye.'' In ji wani mazauni yankin, kodayake kawo yanzu hukumomin tsaro a jihar ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

https://youtu.be/D504h_1x4ws

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng