Gawar da aka binne shekaru 4 yanzu na nan tamkar ta rasu

Gawar da aka binne shekaru 4 yanzu na nan tamkar ta rasu

Marubucin Facebook, Atidade Hassan Abioye,wanda ya garzaya shafin sa bayyana hakan da kuma babu abinda ya sami gangar jikinta

Gawar da aka binne shekaru 4 yanzu na nan tamkar ta rasu

Gawar wata mata da aka birne shekaru 4 da suka wuce a garin Ibadan ya zama abin tattaunawa a cikin jama’a yayin aka same ta tamkar sabuwar gawa babu abinda ya samu likkafanin balle fatar jikinta.

Game da cewar wani marubucin Facebook, Atidade Hassan Abioye,wanda ya garzaya shafin say a daura hotunan gawar bayan an hakota daga cikin kabarinta sakamakon ruguza gidajen da akeyi a inda aka birne ta ,domin ginin hanya.

KU KARANTA: Karban bashi: Ba zan ja da Sanatoci ba-Shugaba Buhari

Atidade Hassan Abioye yace: “Abin mamaki,Allah da girma yake. Ga wata mata wacce ta rasu tun shekarar 2012 kuma aka birne ta . a yanzu, gwamnati tana shirin gyara wasu wurare a Ojoo kuma zai bukaci rusa wasu gidaje da shaguna. Amma abin mamakin shine akwai wata maa da ya kamata a hako kabarin ta saboda a gina hanyar da kyau,kawai sai aka ga gawan kamar yadda birne ta, babu datti a likafannin ta, likafannin na kwance,Allah ya tsare jikinta. Lallai akwai Aljanna da jahannama, ka kasance mai gaskiya kuma ka dinga kyautata ma makwabta. Abun mamaki ne anan. Allah da girma yake  kuma muna imani da shi da manzon sa (tsira da mainci Allah su tabbata a gareshi).

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: