Abin da ya sa na shiga Kungiyar shan jini
- Wani dan Kungiya shan jinni da aka kama ya bayyana abin da ya shiga cikin Kungiyar
- Yace jarin kasuwanci yake nema shiyasa ya shiga wannan Kungiya
- Yanzu haka ‘Yan sanda sun kama wannan mutumi
Jami’an ‘Yan Sanda sun kama mutane 12 da ake zargi ‘Yan Kungiyar Shan jini ne a Unguwar Apo da ke Birnin Abuja. An kama wadanna mutane da bindigogi, da adda da wukake Inji Jaridar Punch. Ana zargin wadannan mutane suna cikin wata Kungiyar shan jini mai suna Norsemen.
Kowane daga cikin wadanda aka kama ya bayyana dalilin da ya sa ya shiga wannan Kungiyar shan jini. Wani daga cikin su mai suna Fidelis Ogabor yace ya shiga Kungiyar shan jini ne domin karbar bashin kudi, Mista Ogabor yace yana neman kudi N200, 000 ne domin ya bude shagon gyaran gashi.
KU KARANTA: Za a hana bara a Najeriya
Mista Ogabor yace an kore sa ne daga wurin aiki, hakan ta sa ya shiga wannan Kungiyar shan jini. Bayan ya nemi taimakon kudi daga wani Mista Williams, sai yace masa sai da ya shiga Kungiyar shan jini na Norsemen idan yana bukatar a taimaka masa.
Fidelis Ogabor yace ya samu aron kudin bayan ya shiga Kungiyar shan jini, sai dai da ya gaza biyan bashin, ‘Yan Kungiyar shan jini sun tura ‘yan iskan gari suka likida masa dan-karan duka. Bayan nan ne ‘Yan Sanda suka kama sa, aka ce yana cikin ‘yan Kungiyar shan jini.
Asali: Legit.ng