Dan wasar Brazil mai tarihi Alberto Carlos ya mutu
Carlos Alberto, Kaftin din kasar Brazil wanda ya jagoran cesu zuwa cin kofin duniya a kasar Mexico 1970 ya mutu.
Carlos Alberto a hannun hagu a tsaye a cikin yan wasar Brazil da suka ci kofin duniya a shekara ta 1970.
Dan wasan da ake tunanin yafi kowane dan wasa iya tsaron baya tun a lokacin har zuwa yau, ya mutu sanadiyar ciwon zuciya.
A shekara ta 1970, kwallo da ya zura ma kasar Italy, yana 1 daga cikin kwallaye masu kayatar wa da aka jefa a wasannin da ake doka wa na cin kofin duniya.
Tsohon dan wasan Santos da Fluminense ya doka ma kasar Brazil wasa har sau 53, kuma ya ci kofuna da kungiyoyi daban daban.
Ya doka wasa fiye da 400 a matsayin dan wasa kwararre.
Sunan Alberto ya fito a rukunin sunayen yan wasa kwararru na cin kofin duniya na karni na 20, da kuma mutane 100 rayayyu masu kwarewa a kwallo a shekara ta 2004.
Bidiyon tsohon Kaftin Super Eagles mai suna Stephen Keshi
Asali: Legit.ng