Jakadiya ta ki amincewa da zabin saboda rashin lafiyan mijinta

Jakadiya ta ki amincewa da zabin saboda rashin lafiyan mijinta

- An rahoto cewa daya daga cikin jakadan da aka zaba, Dame Pauline Tallen ta ki amincewa da zabin nata

- Tallen wata mamba a kungiyar amintattu na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), ta ki amincewa da nadin jakadanci da akayi mata saboda mijinta

- Ta yi godiya ga shugaban kasa da kimanta ta da yayi don ta bauta wa kasar Najeriya a matsayin jakadiya

Daya daga cikin jakadan da aka zaba kuma tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Plateau, Dame Pauline Tallen ta ki amincewa da zaban ta da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi domin ta zama jakadiyar kasar.

Jakadiya ta ki amincewa da zabin saboda rashin lafiyan mijinta
Pauline Tallen ta ki amincewa da nadinta a matsayin jakadiya saboda rashin lafiyan maigidan ta

Pauline Tallen wata mamba ta kungiyar amintattu na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), ta ki amincewa da nadin a matsayin jakadiya saboda ta kula da mijinta mara lafiya.

KU KARANTA KUMA: Kada ka tattauna da shugabannin Niger Delta- NDA ga Buhari

Tsohuwar mataimakin gwamnan a wata sanarwa da ta rubuta a shafin zumunta na Facebook, tace ta gode kimanta ta da shugaban kasa yayi domin ta bauta wa Najeriya a matsayin jakadiya.

Mu tuna cewa kimanin watanni biyu da suka wuce lokacin da ake tattance daya daga cikin jakadun da aka zaba, Vivian Okeke ta samu matsala lokacin da aka bukaci ta yi wakan kasa (National Anthem) a gaban mutanen da suka taru.

Mrs Okeke ta kasa karanta sashin karshe amma Sanata James Manager, wani mamba na kwamitin ya taimaka mata.

Kalli bidiyon a kasa:

https://youtu.be/exOqC_j3iUs

Asali: Legit.ng

Online view pixel