Wani mutum ya kama maciji

Wani mutum ya kama maciji

Me zaka yi in kana son kama katon maciji, wanda ke boye a cikin katon rami? Wadan nan mutanen sun kirkiro hanya mai hadari da mamaki. In kaga abunda suka yi zaka dauke su mahaukata.

Kana bukatar abinci ko kana son cire katon maciji a bayan gidan ka? Wannan ita ce da ta dace kabi!! Wadan nan mutanen sun tafi farauta, amma basu tafi da wani makami ba, amma da suke da shi a matsayin makami shine tsumma, da wata wuka mai kaifi, sai kafafun su.

Wani mutum ya kama maciji

Eh, haka ne, lalle kafar mutum ce, duk da yake dai daya daga cikin mafarautan yafi saka kansa cikin hadari fiye da sauran, ya shafa wani mai a kafar shi, sai ya daure da tsumma, sai yazo ya saka kafar sa a cikin ramin katon macijin.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta nemi da a sa doka dan samun wani kaso

Wani mutum ya kama maciji

Ramin yana da girman da kusan rabin mutum ze iya shiga, sauran mafarautan sun jirashi a waje dan su ciro shi kuma su fito da macijin.

Bayan kankanin lokaci wani abu ya faru, mutumin yayi ihu, suka ciro shi daga ramin, abunda suka gani shine jini na tartsi da kafar mutumin, katon macijin mai tsawon mita 5 ya cinye tarkon kuma ya hadiye kafar mutumin har zuwa guiwa.

Wadan nan mutanen sun saka kansu cikin hadari dan kama dan kama katon maciji, kuma sun fidda shi daga ramin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng