An yiwa mata bulala a bainar jama'a
- An yiwa wata mace bulala 23 a gaban jama’a a bisa laifin aikata laifukan da suka sabawa shari’ar musulunci
- An kuma yiwa wasu karin mutane 13 a gaban jama’a haddi a gaban jama’a a bisa laifukan taba juna da runguma da ire-irensu
Matar wacce aka boye sunanta an durkusar da ita a gaban jama’a an kuma yi mata bulala tara ne a bisa umarnin shari’a.
An dai zartar da hukuncin ne a wani masallachi a babban yankin Banda Aceh na kasar Indonesia a ranar Litinin 17 watan Oktoba.
Matar da kuma wasu mutane 13, maza 7 da kuma wasu matan 6, masu shekaru tsakanin 21 da 30 an zartar musu da hukuncin bulalar ne sakamakon aikata wasu laifuka daban-daban na samartaka da suka sabawa sharia’ar musulunci.
A cewar rahotanni daga kafofin yada labarai a yankin, kowannensu an yi masa bulala tsakanin guda tara da kuma 25 gwargwadon girman laifin mutum.
Sai dai kamfanin dillancin labarai na Antara na kasar ya ce, an same su ne da laifukan da suka kama daga rige hannun juna, da shafe-shafe, da rungumar juna, da sumbata, da kuma yin zina alhalin basu da aure, an kuma jinkirtawa mace ta cikon 14 hukuncin bulalar, saboda da tana dauke da juna biyu har sai ta haihu.
KU KARANTA KUMA: Ra’ayi: Shin Buhari zai kai labari kuwa?
Zainal Arifin, mataimakin Magajin garin Yankin, dangane da hukuncin ya ce, “ba yau muka saba zartar da hukuncin bulala a wannan gari na Banda Aceh ba, wanda kuma hakan na nuna cewa gwamnati da kuma al’ummar yankin sun yi tsayin daka wajen tabbatar da Shari’ar Allah.”
Yankin Aceh shi ne kadai yankin Indonesia 34 da ke aiwatara da shari’ar musulunci a kasar da ke da yawan al’ummar musulmai, bugu da kari aikata zina, da luwadi, da shan giya, da caca, da sauran laifukan da musulunci ya hana, kotunan Musulunci na kasar ne ke yanke hukunci, ciki har da yin bulala ga mata da maza a bainar jama’a.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta sha yin kira da daina yiwa jama’a bulala a kasar, tana mai cewa, hakan karan tsaye ne ga dokokin kasa da kasa, da kuma kundin tsarin mulkin kasar Indonesia wadanda suka haramta azabtarwa da kuma keta hakkin bil adama.
Asali: Legit.ng