Rabon Gado: Wani malami ya ja kunnen Sanatocin Najeriya
– Wani Babban Malami a Kasar nan ya ja kunnen Sanatocin Najeriya game da kudirin rabon gado
– Dr. Muhammad Sani Rijiyar-Lemu ya gargadi Sanatoci game da yunkurin raba kason gadon maza daidai da mata
– Malamin yace wannan ya sabawa addinin musulunci kuma tsokanar fada ce
Wani Babban Malamin Musulunci Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar-Lemu ya gargadi Sanatocin Najeriya game da yunkurin kawo wata doka da za ta sa rabon gadon namiji ya zama daidai da na diya mace a Kasar nan. Wata Sanata mai suna Abiodun Olujimi daga Ekiti ta kawo wannan kudiri.
Babban malamin da ke Kano yace wannan doka ta sabawa Addinin musulunci, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar-Lemu yace akwai yi wa Addinin Musulunci Karen-tsaya da kuma tsogala a wannan kudiri. Malamin yace akwai yadda shari’a ta tsara rabon gado a addini cikin Hikima kuma babu yadda za ayi a canza wannan.
KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya gargadi Sanatocin Najeriya
Wannan malamin ya kira Musulman Sanatocin Najeriya da ke Majalisar da kar su amince da wannan kudiri. Tun a ranar farko dai wani Sanata Kirista mai suna Emmanuel Bwacha yace hakan ya saba addinin Kiristanci.
A baya wani Shehin Malami a Kasar nan Sheikh Dahiru Bauchi yayi kira ga Sanatocin Kasar da su bi a sannu game da abubuwan da suka shafi addini a Kasar. Sheikh Dahiru Bauchi yace musulunci ya tsara ka’idar rabon gado a Kur’ani. Kungiyar Izala ta JIBWIS ma dai tace ba za ta yarda ba.
Ku kalli wani bidiyo na zanga-zangar da mata sukayi kan Bukola Saraki da Ike Ekweremadu:
Asali: Legit.ng