Dan baiwa: Tun kafin ya cika shekara ya fara tafiya da magana
– Ga wani yaro dan baiwa da ya fara fede mutum tun yana dan shekara bakwai kacal a duniya
– Tun yana kuma wata goma da haihuwa ya fara iya magana da kuma tafiya, yana shekara biyu ya fara rubutu
– Akrit Jaswal dan baiwa ne, tun yana dan shekara biyar ya fara karanta littatafan Shakespeare
Ga wani yaro dan baiwa mai suna Akrit Jaswal, asalin wannan yaro dan Kasar India ne. Jaswal ya fara iya magana tun kafin ya cika shekara daya a duniya, tun dai yana wata goma ya fara ta-ta-ta ya kuma fara surutu. Yayin da Akrit ya cika shekara biyu a duniya kuwa ya fara karatu da rubutu.
Tun wannan yaro dan baiwa yana da shekaru biyar rak a duniya kuwa ya fara karance-karance littatafan Shakespeare. Akrit dan baiwa yana da karfin kwakwalwa maki 146, abin da ake kira IQ, duk Kasar India dai babu mai irin wannan kwakwalwa. Kasar India tana da mutane fiye da Biliyan daya.
KU KARANTA: Najeriya za ta dauki malamai 200000 aiki
Ai lamarin wannan yaro ya wuce nan, tun yana dan shekara bakwai a duniya yayi abin da ba a taba yi ba a Tarihi. Jaswal dan baiwa ya fede wata yarinya, ya kuma hada ta tsaf. Wannan yarinya ‘Yar shekara takwas ta kona hannuwan ta, inda yatsun ta suke like, amma Akrit da yake dan baiwa ne, yayi mata aiki ya raba yatsun tun yana dan shekara bakwai.
Tun yana dan shekara 12 dai ya fara karatun sa na Digiri, abin da ba a taba samu ba a Yankin su. Yanzu haka yana karatun sa ne a fannin Biomedical Engineering a Jami’ar IIT Kanpur. Dan baiwa Jaswal y adage sai ya nemo maganin cutar Cancer.
Asali: Legit.ng