'Yan Najeriya na fadin ra'ayinsu kan jawabin A'isha Buhari
-Hajiya Aisha Buhari ta fasa kwai da kuma tayi magana akan hayaniyan da ke faruwa cikin jam’iyyar APC.
Uwargidan shugaban Najeriya, uwargida A'isha Buhari tace mutane sun fara kawo baraka cikin All Progressive Congress (APC)
A wata hira da gidan radiyon BBC sashen Hausa wand aka dan tsakuro ma jama'a ranar Talata 11 ga Oktoba, tace maigidanta bai san mafi yawan mutanen da ya nada cikin gwamnatinsa ba. 'Yan Najeriya na Tofa albarkacin bakinsu inda wasu ke cewa jawabin A'isha Buhari sheda ce akwai matsala cikin gwamnatin Buhari. Wasu kuma suna cewa wannan ba wani na fadin abinda ta fada a bayan fage.
KU KARANTA:Rashin motar asibiti ya sanya wasu iyaye sun dauki gawar ‘yarsu a kurar ruwa
Da aka tambaye ta ko maigidanta ya san mutanen da ke tsakkiyar cece-kucen da ake ciki, tace: "Ko ya sani, ko bai Sani ba, wadanda suka zabe shi sun sani. Yana iya gani, kuma idan ka tambaye shi cikin mutane 50 da ya zaba, bai san 45 daga cikinsu. Ni ma ban sansu ba cikin shekaru 25 da nayi tare dashi.
Asali: Legit.ng