Dailin da yasa Arewa suka juya ma Jonathan baya

Dailin da yasa Arewa suka juya ma Jonathan baya

- Odia Ofemun yayi game da sake fasalin al’amuran Najeriya

- Mawakin yace ya yaki da mai ne dalilin daya Jonathan ya samu matsala da Arewa

- Ya Lura cewa yarjejeniya masu zaman kansu kar su sha kan kundin tsarin mulki

Odia Ofeimun ya bayyana cewa dalilin da yasa Arewa ta ki Goodluck Jonathan a zaben shekara ta 2015 ya kasance saboda kungiyar mai.

A wata hira da jaridar Vanguard, Ofeimun ya maganta gameda al’amarin sake fasalin al’amuran kasar da kuma yadda Najeriya ta kai zuwa yanzu.

Ofeimun ya kuma maganta kan matsalar da Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samu da Arewa cewa saboda man petir ne.

KU KARANTA KUMA: Motan yan fashi yayi hatsari

Dailin da yasa Arewa suka juya ma Jonathan baya
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Yace: “Bari mu sa hannu a ciki: ba wai kawai saboda wani yarjejeniya da akayi a cikin jam’iyyar PDP na cewa dan Arewa zai ci gaba da mulki daga Umaru Musa Yar’adua bane. Koda ace akwai wani yarjejeniya masu zaman kansu a jam’iyyar siyasa bai kamata a dauke ta da muhimmanci fiye da kundin tsarin mulkin kasa ba.”

Ya bayyana cewa matsalar mai shine ainahin dalilin da yawo kiyayyar Arewa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan har ta kai suka juya masa baya a zaben shekara ta 2015. Har ta kai yan Arewa da dama suka sauya sheka daga jam’iyyar.

“A lokacin da shugaba Jonathan ya nemi gyara alakarsa da Arewa, ta hanyar daura matsayi da ayyuka a Arewacin kasar, don dawo da yawan wadanda suka bar jam’iyyarsa, shugaban kintsa abun tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya warware masa tsakar sa.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng