'Karin Bayani: An dakatar da 'yar tseren Najeriya, Blessing Okagbare, na shekaru 10
- Sashen Kula da Halayen 'yan wasa na Athletics Integrity Unit (AIU), ta dakatar yar tseren Najeriya Blessing Okagbare na tsawon shekaru 10
- AIU ta dauki wannan matakin ne bayan gwaje-gwaje da bincike da aka yi ya nuna Okagbare tana shan haramtattun sinadaren kara kuzari
- An dakatar da Okagbare na shekaru biyar saboda amfani da haramtaccen sinadarin sannnan shekaru biyar kuma saboda kin bada hakin kai yayin bincike
An dakatar da yar wasar Najeriya, da ta ci azurfa a gasar dogon tsalle a wasan Olympics na 2008, Blessing Okagbare, saboda amfani da kwayoyin kara kuzari, Sashen Kula da Halayen 'yan wasa na Athletics Integrity Unit (AIU), ta sanar ranar Juma'a.
An dakatar da 'yar shekaru 33, wacce kuma yar tsere ce daga gasar Tokyo Olympics a bara kafin wasar kusa da na karshe na tseren mita 100 na mata bayan gwaji ya nuna ta sha sinadarin kara kwazo a Slovakia a ranar 19 ga watan Yuli.
Wani sashi na sanarwar da AIU ta fitar ya ce:
"Kwamitin ladabtarwa ya dakatar da yar tseren Najeriya Blessing Okagbare na tsawon shekaru 10.
"Shekaru biyar na gano cewa tana shan sinadaren da aka haramta na kara kwazo sai kuma shekara biyar saboda rashin bawa kwamitin bincike na AIU hadin kai a lokacin da suke bincikar ta."
Ana zargin mai magani yar Texas, Eric Lira ce ta taimakawa Okagbare
A takardar tuhumar da aka gabatar kan wata mai magani yar Texas a Amurka mai suna Eric Lira a watan da ya gabata, ba a ambaci Okagbare da sunanta ba.
Sashi shari'a a Amurka a New York ya ce Eric Lira, yar shekara 41 'mai bada magunguna mazauniyar El Paso, ce ta samarwa yan tsere biyu kwayoyi da nufin 'gabatar da rashawa a gasar Tokyo Games'.
Takardar tuhumar ta kuma bayyana sakon kar ta kwana a tsakanin Okagbare da Eric inda ta ke sanar da ita cewa ta ga amfanin kwayayin a yayin da ta yi tseren 100m a gwajin Olympics a Legas.
Daga bisani kuma akwai sakon da Okagbare ta tura wa Eric inda ta ke fada mata cewa fa akwai matsala domin gwajin da aka yi mata ya nuna ta sha sinadarin HGH.
Daga karshe takardar korafin ta nuna cewa Blessing Okagbare ce Athlete 1 da ake boye sunanta.
Asali: Legit.ng