NFF ta zauna da Mourinho mai karban N2bn a shekara a kan batun zama kocin S/Eagles
Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick yace su na cigiyar sabon koci
Ana neman kwararren mai horas da ‘yan wasan da zai jagoranci ragamar ‘yan kwallon Super Eagles
Pinnick yace sun yi kokarin dauko hayar irinsu kocin AS Roma, Jose Mourinho mai albashin N2bn
Jaridar Punch ta rahoto Mista Amaju Pinnick ya na bayani a lokacin da ya zanta da wasu manema labarai a ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, 2021.
Da yake hira da ‘yan jaridan a garin Legas, Amaju Pinnick ya tabbatar da cewa hukumar NFF za ta nemi sabon kocin ‘yan kwallon kasar nan ba da dadewa ba.
Shugaban na NFF yace sun zauna da Serbian Mladen Krstajic da Jose Mourinho a yunkurinsu na neman kwararren kocin da zai rike tawagar Super Eagles na kasar.
“Mun yi magana da to Mladen (Krstajic) amma bayan nay a samu aiki da Maccabi Tel Aviv. Haka Jose Mourinho, ba zan ce maku ba mu yi magana da shi ba.
“Ni da Ministan wasanni mun yi magana da Mourinho, kuma babu wata matsala yin hakan.” - Amaju Pinnick
Za a iya dauko hayar Mourinho?
Jose Mourinho ya na cikin masu horas da ‘yan wasan da suka fi shahara a Duniya. Mourinho ya yi aiki da Chelsea, Real Madrid, Inter Milan da Manchester United.
Rahoton Republic World yace albashin Jose Mourinho duk shekara ya kai kimanin fam miliyan €4m zuwa €7m. Sama da Naira biliyan biyu kenan a kudin Najeriya.
Wanene ya fi dacewa da Super Eagles? - NFF
Pinnick ya kuma shaidawa manema labarai cewa Jose Peseiro ya na cikin wadanda suke hari. Peseiro ya taba aiki da Real Madrid, yanzu shi ne kocin FC Porto.
Shugaban na NFF yace abin da suke nema shi ne kocin da zai iya horas da ‘yan wasa da kyau. Abu na biyu a nemi wanda yake da kwadayin cin kofi da tawagar.
Austin Eguavoen zai je AFCON 2022?
Daily Post tace hakan ya na nufin Austin Eguavoen ba zai samu damar da zai jagoranci ‘yan kwallon kafan Najeriyan a gasar AFCON da za ayi a 2022 ba.
Najeriya ta na cikin kasashen da za su kara a kasar Kamaru a gasar cin kofin nahiyar Afrika.
Ku na da labari cewa yanzu Austin Eguavoen ne mai horas da ‘yan kwallon Najeriya na rikon kwarya tun bayan da hukumar NFF ta salami Gernot Rohr.
Eguavoen ya taba zama gwarzon nahiyar Afrika a 1994, kuma ya yi shekaru a matsayin kyaftin din Super Eagles. Kocin zai yi aiki tare da su Joseph Yobo.
Asali: Legit.ng