Zidane da kwararrun koci 5 da ake ganin za su iya maye gurbin Ole Solskjaer a Old Trafford
- A jiya ne kungiyar Manchester United ta sallami Ole Gunnar Solskjaer bayan wasanta da Watford
- An fara kawo sunayen wasu masu horaswar da za a iya yi wa tayin kujerar da Ole Solskjaer ya bari
- Akwai yiwuwar tsohon kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya karbi aikin horas da 'yan wasan kungiyar
Manchester - Ba sabon labari ba ne cewa an sallami Ole Gunnar Solskjaer daga aikin horas da ‘yan wasan kungiyar Manchester United a karshe makon jiya.
Tuni har an fara maganar wanane zai maye gurbin da Ole Gunnar Solskjaer ya bari a Manchester.
A wannan rahoto, mun kawo wasu daga cikin masu horaswar da za ayi wa tayin horas da ‘yan kwallon kafan kungiyar Manchester United a halin yanzu.
Jaridar Marca ta kasar Sifen tace Zinedine Zidane yana cikin wadanda ake rade-radin zuwansu Manchester. Haka zalika ana tunanin kawo Erik ten Hag.
1. Zinedine Zidane
Wanda yake kan gaba shi ne tsohon kocin Real Madrid, Zinedine Zidane, wanda a cikin ‘yan shekaru ya lashe kofuna da-dama, daga ciki akwai gasar cin kofin nahiyar Turai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sauran kofunansa sun hada da LaLiga Santander biyu, Supercopa de Espana biyu, da UEFA Super Cups.
2. Brendan Rodgers
Kocin na Leicester City, Brendan Rodgers ya shiga bakin magoya-baya ganin irin abin da ya tabuka da yake rike da kungiyoyin Swansea City, Liverpool da kuma Celtic a baya.
3. Michael Carrick
Har ila yau akwai sunan Michael Carrick a cikin wanda jaridar ta kawo. Kamar Solskjaer, tsohon ‘dan wasa Carrick zai iya zama babban kocin kungiyar na din-din-din idan ya dace.
4. Erik ten Hag
Wani koci da ake tunani zai iya zuwa Manchester United bayan tafiyar Ole Solskjaer shi ne Erik ten Hag wanda ya ke abin a –yaba da kungiyar Ajax da yake horaswa tun a 2017.
5. Laurent Blanc
Rahoton yace tsohon ‘dan wasan Man Utd, Laurent Blanc yana iya dawowa, ya hadu da Edison Cavani. Blanc ya horas da kungiyoyin Bordeaux da PSG da kuma kasar Faransa.
Ole Gunnar Solskjaer ya yi waje
A ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamba, 2021, aka tabbatar da cewa an sallami Ole Gunnar Solskjaer daga aikinsa na horas da 'yan wasan kungiyar Manchester United.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na yanar gizo da a Instagram a safiyar jiya, tace ya zama dole ta dauki wannan mataki ma ciwo.
Asali: Legit.ng