Man United ta sha da kyar bayan Ronaldo ya kuma kawo agaji daf da za a tashi wasan UCL
- Cristiano Ronaldo ya taimakawa kungiyar Manchester United ta tashi kunnen doki da Atalanta dazu.
- ‘Dan kwallon ya ceci kungiyarsa a birnin Bergamo kamar yadda ta kaya da suka gwabza a Manchester.
- A halin yanzu Ronaldo ya ci wa Manchester United kwallaye 9 bayan dawowarsa kulob din a kakar 2021.
Bergamo - Cristiano Ronaldo ya sake zama gwarzo a yayin da kungiyarsa ta Manchester United ta kwaci kanta da kyar a hannun Atlanta a gasar Turai.
BBC tace Manchester United tayi kunnen doki da kungiyar Atalanta a wasan da ta buga a ranar Talata. Hakan ya sa ta ke matsayi na daya a rukuninta.
Ronaldo ya jefa kwallo a raga bayan ‘dan kasarsa Bruno Fernandes ya kawo masa kwallo. A wasan jiyan ma Ole Solskjaer ya yi watsi da tsarin 4-2-3-1.
A lokacin da wasan ke shirin zuwa karshe, Ronaldo mai shekara 36 ya jefa kwallo na biyu a ragar Juan Musso, kamar dai yadda ta faru a Ingila kwanaki.
Josip Ilicic da Duvan Zapata suka ci wa Atlanta kwallaye a gaban magoya bayanta a filin wasan Gewiss.
Ronaldo ya sha gaban Solskjaer bayan ya cece shi
Goal.com tace wadannan kwallaye da Cristiano Ronaldo ya ci, sun sa ya sha gaban Ole Gunnar Solskjaer a yawan kwallayen da suka ci wa kulob din.
Ole Gunnar Solskjaer tsohon ‘dan wasan gaba ne da ya bugawa Manchester United kwallo, kocin ya ma yi kwallo tare da Ronaldo tsakanin 2003 da 2007.
A halin yanzu Ronaldo ya ci kwallaye 127 da rigar Manchester United a wasanni 303 da ya buga. Gwarzon Duniyan yana da kwallaye 139 a gasar kofin Turai.
Atalanta: Me Manchester United take cewa?
Da aka tashi, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa sun ci sa’a ne a hannun Atalanta a kasar Italiya. ‘Dan kwallon yace ya yi murna domin wasan ya yi zafi.
A na sa jawabin bayan wasan, koci Ole Gunnar Solskjaer ya yabawa Ronaldo mai kwallaye tara a wasanni 11 a bana, da sauran ‘yan wasan da ba su cire rai ba.
An tasa Ole Gunnar Solskjaer a gaba
Kwanaki kun ji cewa ana ta rade-radin Manchester United ta fara lissafin sallamar Ole Gunnar Solskjaer bayan cin mutuncin da Liverpool ta yi wa Manchester.
Liverpool ta je har gida ta doke Manchester duk da cefanen da kungiyar ta yi. Tun da Solskjaer ya karbi ragamar kungiyar a karshen 2018, bai taba cin wani kofi ba.
Asali: Legit.ng