Yan Yahoo
Wasu ƴan damfarar yanar gizo da aka fi sani da Yahoo Boys sun far wa dakarun hukumar EFCC ba zato ba tsammani, sun kashe jami'i ɗaya wani na kwance a asibiti.
'Yan ta’addan Lakurawa sun kai hari a Kebbi, inda suka kashe mutane hudu, ciki har da ma’aikatan Airtel. Kwamishinan 'yan sanda ya nemi karin hadin kan jama’a.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi gwamnati da son boye rahoton gaskiya a kan rashin tsaro, inda ya yi fatan wannan ya zama zargi kawai.
Mansura Isah ta shiga tsananin damuwa bayan 'yan damfara sun sace gaba daya kudin da ta mallaka a asusun bankunanta biyu. Tsohuwar jarumar ta ce yanzu ta talauce.
Malamin addinin Musulunci, Abdulrasheed Alaseye, ya fada cikin damuwa bayan ya rasa N351,169 a hannun kamfanin da ya yi alkawarin samar masa da damar zama dillali.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce kar dalibai su ji tsoron shirinta na gwajin kwaya idan za a fara sabon zangon karatu domin taimaka masu.
Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta ce 'yan damfara sun yi kutse a lambar WhatsApp din gwamnan jihar, Umo Eno inda har suka fara tura sakon neman kudi daga jama'a.
Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta sanar da kama kasurgumin barawo da ya sace makudan kudi da kayayyaki. Za a gurfanar da Glory Samuel a gaban kotu.
Matasa a Akure, da ke jihar Ondo sun gudanar da gagarumar zanga-zanga suna neman hukumar EFCC ta gaggauta sakin wasu da ta kama bisa zargin damfara da kafar intanet.
Yan Yahoo
Samu kari