Albashin ma'aikata
Yayin da Kungiyar Kwadago ta NLC ke takun-saka da gwamnatin Najeriya, mun kawo muku rahoton kasashen Afirka da suka fi biyan mafi karancin albashin ma'aikata.
Awanni kaɗan bayan bullar rahoton sabon mafi karancin albashi, gwamantin tarayya ta musanta cewa an fitar N100,000 a matsayin mafi karancin albashi.
Yayin da Kungiyar NLC ta ke neman karin albashi, Ministan kudi, Wale Edun ya gabatar da sabon tsarin biyan mafi karancin albashi ga Shugaba Bola Tinubu.
A yau Alhamis ne wa'adin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba ministan kudi, Wale Edun kan samar da yadda karin albashi zai kasance a Najeriya ya cika
Mai magana da yawun majalisar wakilai, Hon. Akin Rotimi, ya ce kungiyoyin kwadago suna zuzuta albashin 'yan majalisun tarayya domin harzuka 'yan Najeriya.
Tattaunawar da ake yi tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da 'yan kwadago ta tashi ba tare da an cimma matsaya ba. Za a sake zama domin tattaunawa.
Alamu sun fara karkata kan cewa kungiyar kwadagon kasar nan (NLC) za ta sassauta bukatar mafi karancin albashi daga N494,000 zuwa N100,000 nan gaba.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da wakilan gwamnatin tarayya a tattaunawar da ake yi kan mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya.
Daniel Bwala ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati ta kara tayin da ta yi na za ta rika biyan ma'aikata N60,000a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.
Albashin ma'aikata
Samu kari