Albashin ma'aikata
Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000.
Shugabannin ƙungiyar kwadago sun soki jihohin da ke jan kafa kan albashin N70,000, suna ganin hakan take hakkin ma’aikata ne a wannan mawuyacin lokaci.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar. Gwamnan zai fara biyan sabon albashin daga watan Nuwamba.
Wasu gungun ƴan fansho sun fita zanga zanga a ma'aikatar kudi ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, sun nemi gwsmnati ta biyasu hskkokinsu na tsohon tsarin fansho.
Fasto Umo Eno, gwamnan jihar Akwa Ibom ya ba da tabbacin cewa zai biya ma’aikatan jihar albashi biyu a watan Disamba domin inganta bukukuwan Kirsimeti.
Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana shirinta na rike albashi da alawus alawus na ma'aikatan da ba su mallakin lamɓar zama cikakken mazaunin jiha ba.
Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta shirya fara yajin aiki a jihohin da ba su fara biyan sabon mafi karancin albashi ba. Ta ba gwamnonin jihohin wa'adi.
Wasu gwamnoni a jihohin Najeriya har yanzu ba su fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi ba. Jihohin sun hada Zamfara, Taraba da Sokoto.
Gwamnatin jihar Borno ta fara biyan malaman makarantun firamare sabon mafi karancin albashi na N70,000. Malaman makarantan sun nuna farin cikinsu kan hakan.
Albashin ma'aikata
Samu kari