Aikin noma a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da taron masu kananan sana'o'i, wurin noma mai amfani da hasken wutar rana da kuma rabon tallafi ga mazauna Jigawa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gargadi jami'an gwamnatin Kano su guji karkatar da tallafin takin manoman jihar a dukkanin kananan hukumomi 44. Manoma 52, 000 za su samu.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ware Naira Biliyan 29 domin gudanar da ayyukan raya jihar Kano. An ware adadin kudin ne domin aiwatar da sababbin manyan ayyuka.
Majalisar wakilai ta gayyaci wasu daga cikin shugabannin tsaron Najeriya su mata bayani bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya ba sojoji umurnin fara noma.
Mataimakin shugaban majalisar dokokin Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya kaddamar da rabon taki ga manoma a dukkan kananan hukumomin jihar domin bunkasa noma.
Kungiyar mata manoma ta SWOFAN ta bayyana cewa rabon shinkafa kwano ɗai-ɗai ba zai magance yunwa a kasar nan a martani kan iƙirarin gwamnatin na rana shinkafa.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya kaddamar da sabom shirin tallafawa manoma inda ya sanar da age farashin takin zamani zuwa N20,000 duk buhu.
Gwamnatin tarayya ta kara bayani ga a'lumma kan cewa nan gaba kadan farashin kayan abinci zai sauka kasa saboda matakai da ta dauka in ji ministan noma.
Shugaban bankin cigaban Afrika (ADB) Akinwumi Adesina ya ce bude boda domin shigo da abinci zai mayar da Najeriya baya sosai ta bangaren harkokin noma.
Aikin noma a Najeriya
Samu kari