
Aikin noma a Najeriya







Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce zai noma dukkan filayen jihar Nasarawa yayin wata ziyara da ya kai kasar China. Gwamnan zai inganta noma.

Jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya ta kafa tarihin jagorantar noman inabi a Najeriya. Ana samar da kashi 85% na inabin Najeriya a karamar hukumar Kudan ta jihar.

Yayin da yunwa ta addabi al'umma a Najeriya, dan majalisar wakilai, Gboyega Nasir Isiaka, ya ba da shawarar amfani da fasahohin zamani da na gargajiya a noma.

Gwamnatin jihar Jigawa ta kulla yarjejeniyar noma da kamfanin China domin inganta noma. Za a yi amfani da kayan noma na zamani domin yaki da yunwa da talauci.

Farashin shinkafar gida ya ragu da kashi 10 a Enugu; wanda ya sanya mutane farin ciki gabanin Kirsimeti, yayin da dillalai ke ba da shawarar saye kafin ta kara kudi.

Gwamnatin Bola Tinubu ta fara raba tallafin noman alkama a Kano inda ake rage farashin da kashi 75%. Manoma sun yi godiya ga gwamnati a kan lamarin.

Majalisar Wakilai ta fara bincike kan rashin kawo tarakta 2,000 da injinan noma 100, da darajarsu ta kai N111.8bn duk da kashe kuɗi don inganta tsaron abinci.

Gwamnatin Bola Tinubu ta saka tallafin kashi 50 ga masu noman alkama wajen sayen taki da tallafin kashi 25 wajen sayen iri domin samar da abinci a Najeriya.

Najeriya za ta haɗa kai da Pakistan don bunƙasa noma da samar da horo ga ƙwararru, tare da magance kalubale na tsaron abinci da sauyin yanayi, inji Minista.
Aikin noma a Najeriya
Samu kari