Siyasar Najeriya
Fadar shugaban kasa ta yi wa Atiku Abubakar martani kan cewa zai fito takara a zaben 2027. Ta ce dole Tinubu ya yi shekara 8 kamar Muhammadu Buhari.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya sanar da cewa suna tare da masu kada kuri'a a jihohin Kano da Katsina yayin da ake shirin zaben 2027.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce ADC ta samar da hanyoyin da za ta bi wajen samar da ɗan takara a 2027.
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi magana kan zaben 2027. Atiku ya bayyana dan takarar da zai janyewa a jam'iyyar ADC.
A yau Laraba, 15 ga watan Afrilu, 2026, Atiku Abubakar ya sanar da cewa zaɓen 2027 shi ne karo na ƙarshe da zai tsaya takarar shugaban ƙasar Najeriya.
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Chibuike Amaechi, ya yi magana kan zaben shekarar 2027. Rotimi Amaechi ya ADC shawara kan dan takarar da za ta tsayar.
Shugaban APC Nentawe Yilwatda ya ce ba za a bar masu sauya sheƙa su karɓe ikon jam’iyya ba. Wannan na zuwa ne yayin da wutar rikici ta fara ruruwa a APC.
Tsohon shugaban APC na kasa, Johh Oyegun ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ta shirya kafa gwamnati a babban zaben 2027, ya ce lokacin canji a Najeriya ya yi.
A labarin nan za a ji cewa Maurice Vonobolki ya umarci dukkanin magoya bayansa da ke kananan hukumomin jihar Adamawa da su yi murabus daga jam'iyyar APC.
Siyasar Najeriya
Samu kari