Siyasar Najeriya
Mai magana da yawun jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya ce Rotimi Amaechi ya taɓa barazanar ficewa daga jam’iyyar saboda yadda ake nuna wa Peter Obi fifiko.
Jam’iyyar APC za ta fara zaben fitar da gwani na ‘yan majalisar wakilai a mazabu 360 yayin da manyan ‘yan siyasa ke neman tikitin takara a zabukan 2027 masu zuwa.
Dan Majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Abuja Municipal/Bwari, Hon. Obika ya bayyana cewa ya canza jam'iyya ne saboda cika buri da manufofinsa na siyasa.
Tsohon Ministan sufuri kuma mai neman takarar shugaban kasa a karkashin inuwar ADC, Rotimi Amaechi, ya sha alwashin gyara Najeriya cikin shekara hudu.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zabenshekarar 2027 da ake tunkara a karkashin jam’iyyar APM.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na LO, Peter Obi ya jaddada cewa matukar aka zabe shi a zaben 2027, shekaru hudu kawai zai yi ya mika wa Arewa mulki.
Tsohon shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya janye daga neman takarar gwamnan jihar Yobe a karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Masu neman takara a karkashin jam'iyyar APC a zaben 2027 sun dura ofishin jam'iyyar da gidan shugaban jam'iyyar suna jiran sakamakon tantance su.
Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa Atiku Abubakar da sauran 'yan adawa na taimaka masu. Ya ce yadda suke caccakae juna abin burgewa ne ga APC.
Siyasar Najeriya
Samu kari