Siyasar Najeriya
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya yi ikirarin cewa an tafka magudi a zabukan fitar da gwanin ADC da aka yi, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya caccaki manyan yan adawar Najeriya da suka hada da Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso, ya kira su da makaryata.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya tuna baya kan abubuwan da suka faru da shi kafin ya dare kujerar mulki. Ya bayyana cewa an ba shi kyautar kudi.
Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru ya roki talakawan jihar da su sake zaben jam'iyyar APC a 2027 tare da yafe masu kura kuran da suka tafka a baya.
Wani tsohon ɗan takarar sanata a jam'iyyar LP a Gombe ta Arewa, Ibrahim Adamu Usmanya fice daga cikinta inda ya nuna goyon baya ga takarar Farfesa Isa Ali Pantami.
Tsagin jam'iyyar ADC karkashin jagorancin Nafiu Bala Gombe, ya bayyana dan takarar shugaban kasa a zaben 2027. An zabe shi ne ta hanyar bin tsarin maslaha.
Dan takarar shugaban ƙasa, Seyi Makinde ya ce manufar neman takararsa ba ta samo asali daga son rai ba, sai dai daga buƙatar sake gina amincewar jama'a.
Tsohon gwamnan Anambra, Mista Peter Obi ya bayyana cewa Rabiu Musa Kwankwaso ba zai zama "dan kallo" ba idan NDC ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya godiya da nuna jin dadi bayan nasarar samun tikitin takarar mataimakin shgaban kasa a jam'iyyar NDC.
Siyasar Najeriya
Samu kari