Siyasar Najeriya
A labarin nan, za a ji cewa jagoran NDC na kasa, Henry Seriake Dickson ya zauna da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran jagororin Kwankwasiyya a kan rikicin Kano.
Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce zai gabatar da kudirin wa’adin shekara shida babu tazarce ga shugaban kasa da gwamnoni.
Jigo a jam'iyyar ADC, Dele Momodu ya bayyana cewa Peter Obi ya taba kin amincewa da shawararsa ta hada kai da Atiku, yana mai cewa ya fi shi farin jini a siyasa.
Kakakin kungiyar ACF, Farfesa Tukur Mohammed-Baba, ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rasa gagarumin goyon bayan Arewa tun bayan zaɓen 2023.
A labarin nan, za a ji cewa daya daga cikin manyan 'yan jam'iyyar APC a Kano, Fa'izu Alfindiki ya ce lokaci ya yi da Sanat Rabiu Musa Kwankwaso zai bar NDC.
Shugabannin APC a mazabar Pantami da ke karamar hukumar Gombe aun ce ba su damsaniyar Isa Pantami ya bar jam'iyyar kafin ya shiga PDP har a ba shi takara.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya sake sukar hanyar da Atiku Abubakar ya bi ya samun takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC.
Tsugunne ba ta kare ba tsakanin shugabannin jam'iyyar NDC a Kano da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Sun zarge shi da yin kaka-gida kan komai a jam'iyyar.
Tsohon shugaban DSS, Lawal Daura ya ƙalubalanci tsarin da ADC ta bi wajen fitar da ɗan takarar gwamna a Katsina tare da yin barazanar zuwa kotu idan ba a bi doka ba.
Siyasar Najeriya
Samu kari