Ilmin Sakandare a Najeriya
Gwamnatin Ondo ta ware N634m don biyan kudin WASSCE na 2024/2025 ga dalibai sama da 23,000, da nufin ba 'ya'yan talakawa damar yin karatu ba tare da matsala ba.
Gwamnatin Tarayya ta sanar da soke JSS da SSS, ta kuma gabatar da tsarin karatun bai daya na shekaru 12 wanda zai taimaka wajen inganta ilimi a Najeriya.
Gwamna Dauda Lawal ya amince da ɗaukar malamai 2,000 a Zamfara don inganta ilimi, tare da gina makarantu da samar da kayan aiki ga ɗalibai da malamai.
Ilimi a Arewa Najeriya na cikin mawuyacin hali saboda rashin tsaro, talauci, da al’adu, inda miliyoyin yara musamman mata ke rasa damar zuwa makaranta.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce ya samu nasarori a a bangaren yaki da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta. Ya ce an rage yawansu.
Gwamnatin Neja na tantance malamai don inganta koyarwa. An karrama tsoffin dalibai kamar Abdulsalami da Sani Bello a taron tsoffin daliban GSS Bida.
Gwamnatin Kwara ta ɗauki mataki kan malamar da ta ci zarafin wata 'yar bautar kasa (NYSC), inda aka rage matsayin aikinta tare da tura ta wata makaranta daban.
Majalisar wakilai ta bukaci ma'aikatar ilimi ta duba yiwuwar aiki da harshen uwa a makarantun boko. Hakan zai sa a dawo amfani da Hausa a makarantun Arewa.
Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya amince da biyan kudaden alawus ga shugabannin makarantun sakandare duk wata domin kula da makarantunsu.
Ilmin Sakandare a Najeriya
Samu kari