Sabon Farashin Man Fetur
Kamfanin man fetur na NNPC ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a soshiyal midiya cewa ya zabtare farashin man fetur. Rahoton sabon farashin fetur "ƙanzon kurege ne."
Hukumar kula da kiyaye hakkin masu saye (FCCPC) ta shawarci gwamnatin tarayya ta buɗe iyakokin kasar nan domin shigo da kayan abinci ta halastacciyar hanya.
Gwamnatin tarayya ta ce babu wani gurbataccen man fetur da ake shigowa da shi Najeriya, wanda hakan ya sabawa ikirarin wani jami’in matatar man Dangote.
Rahota ni daga jihar Adamawa sun nuna cewa mutane sun shiga baƙar wahala sakamakon yajin aikin dillalan mai masu zaman kansu (IPMAN), lita ta kai N2000.
Kungiyar dillan mai ta kasa (IPMAN) ta rufe sama da gidajen mai 1,800 a fadin jihohin Adamawa da Taraba saboda Kwastam ta kwace motocin dakon man mambobinta.
Matsakaicin farashin man fetur a watan Mayun 2024 ya kai N769.62, wanda ke nuni da karuwa idan aka kwatanta da farashin da aka saye shi a watan Mayun 2023 (N238.11).
Tsohon Ministan ayyuka, Babatunde Fashola ya ce ma’aikatan Najeriya na bukatar gwamnati ta biya su albashin da zai isa su gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu taushi ‘yan Najeriya da cewa ba a kasar nan kadai ake shan wahala ba, sauran kasashen duniya na fuskantar irin yanayin.
Shugaban Ɗangote Group, Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana shirinsa na ƙara yawan man fetur ɗin da matatarsa za ta iya ajiyewa daga 4.78bn zuwa 5.3bn.
Sabon Farashin Man Fetur
Samu kari