
Yan fashi







Sojoji sun fatattaki 'yan fashi da makami da suka tare hanyoyi a jihar Kaduna suna kokarin sace mutane. 'Yan fashin sun firgita sun tsere, an ceto mutane biyu.

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun tafka barna a jihar Yobe. 'Yan bindigan sun hallaka jami'an 'yan sanda guda biyu har lahira.

Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana damuwa kan tabarbarewar tsaro, inda ya bayyana yadda suke samun kudade domin ayyukansu.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama 'yan fashi da makami sun tare hanya a tsakiyar birnin Kano suna sace sacen wayoyi. Za a gurfanar da su a kotu.

Atsi Kefas, 'yar uwar gwamnan Taraba, Kefas Agbu ta mutu bayan harin 'yan bindiga da ya rutsa da ita, yayin da take jinya a wani asibiti a Abuja.

Rahotannin sun yi ta yawo cewa an kai wani a hanyar Wukari-Kente a jihar Taraba inda ake zargin an raunata mahaifiyar Gwamna Agbu Kefas da kanwarsa.

Rundunar yan sandan Kano ta kama yan fashi da makami da suka addabi jihohin Arewa. Yan fashin suna tare hanya a jihohin Kano, Bauchi da Jigawa domin sata.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kama wasu mutane hudu da suka yi fashi da makami a jihar Edo. An kama yan fashi da makamin ne bayan sun sace kayan miliyoyi.

Mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya zargi cewa mafi yawan makaman da ke yawo a hannun bata-garin mutane a kasar nan mallakin gwamnati ne.
Yan fashi
Samu kari