Haduran mota a Najeriya
Kungiyar kwallon kafa ta Besiktas ta tabbatar da mutuwar mahaifin dan wasanta kuma kyaftin din Super Eagles ta Najeriya a hatsarin mota a jihar Delta.
Za a yi jana’izar abokan Anthony Joshua biyu da suka rasu bayan hatsarin mota a Najeriya, an shirya sallar a Masallacin London ranar Lahadi, 4 ga Janairu 2026.
Rahotanni sun nuna cewa ma'aikatan NTA shida da wasu mutum daya dan jarida sun mutu a hanyar dawowa daga wurin daura aure a titin Gombe zuwa Yola.
Mutane 7 daga ƙauyen Lawanti a Gombe sun rasu a hatsarin mota kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri yayin da suke kan hanyar zuwa biki, in ji Gwamna Inuwa Yahaya.
Tankar mai ta buge ayarin motar Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a Ibadan, inda ta kashe wani jami’in da ke tare da su, Ibrahim Hussaini.
Tsohon dan Majalisar tarayya daga jihar Ribas, Hon. Ogbonna Nwuke ya tsallake rijiya da baya a hatsarin da motarsa ta kama da wuta a birnin Fatakwal.
Wata tankar man fetur ta yi hadari a Auchi jihar Edo. Wuta ta tashi kuma jama'a da dama sun jikkata bayan fetur ya kwalala zuwa gidaje da shaguna.
Hatsarin mota ya kashe mutane shida a titin Awka–Onitsha da ke jihar Anambra bayan karo tsakanin tipa da bas da ke dawowa daga jana’iza a jihar Ebonyi
An tabbatar da mutuwar matasa 16 da ke shirin fara bautar kasa watau NYSC a hatsarin mota yayin da suke hanyar zuwa sansanin daukar horo a jihar Gombe.
Haduran mota a Najeriya
Samu kari