Haduran mota a Najeriya
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da faruwar wani hatsari wanda ya lakume rayukan wasu mutane shida 'yan gida daya. An ce mota ce ta kwacewa direba.
Ana fargabar mutane hudu da suka hada da wata mai shayarwa sun mutu a Gusau, jihar Zamfara bayan da wata motar tirela ta murkushe su a lokacin da suke kan babura.
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja sun nuna cewa tankar mai maƙare da fetur ta fashe ta kama da wuta a Maitama da ke birnin tarayya Abuja, mutane sun ji raunuka.
An yi mummunan hadarin mota a jihar Ogun inda mutane 18 suka kone kurmus bayan motar ta kama da wuta. Matukin motar na kwance a asibiti saboda raunuka.
A wannan labarin, gwamnan Kaduna, Uba Sani ya mika ta’aziya ga iyalan wadanda su ka rasu a hadarin mota da ta afku a Saminaka da ke karamar hukumar Lere.
Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla mutane 36 sun rasa rayukansu yayin halartar bikin Maulidi bayan mummunan hatsarin mota a Lere da ke jihar Kaduna.
Rundunar ƴan sanda reshen jihar Ogun ta tabbatar da ɓatan wasu mutum w bayan jirgin ruwan da suke ciki ya kife, ta ce ana ci gaba da koƙarin lalubo gawarsu.
Wani mummunan hatsarin mota ya auku a kan titin hanyar Zaria zuwa Kano. Hatsarin ya yi sanadiyyar rasuwar mutum tara yayin da wasu mutum uku suka raunata.
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Ondo , ta tabbatar da aukuwar wani mummunan hatsarin mota wanda ya salwantar da rayukan mutum16.
Haduran mota a Najeriya
Samu kari