Rikicin Ma'aurata
Gwamnatin jihar Ebonti ta hannu mai dakin Gwamna Francis Nwifuru ta fara rabawa zawarawa tallafin gidaje domin su samu wurin zama a kananan hukumomi 13.
Wani magidanci ya kama matarsa a gado sintur tare da wani namiji a ƙasar Zambia, ya ce ya so ba matarsa mamaki ne amma ya taras da abin bakin ciki a gidansa.
Jami'an tsaro sun cafke wani matashi kuma.magidanci, Yayu Musa bisa zargin halaka mahaifiyar matarsa, Ummi a jihar Kogi, ya yi bayanin yadda abin ya faru.
Rundunar ƴan sanda ta cafke wata amarya da ba ta wuce watanni ɓiyar da aure ba bisa laifin garkuwa da kanta a jihar Delta, ta ce bashi ta ci lokacin aurenta.
Rundunar ƴan sanda ta cafke wata mata yar shekara 35, Hadiza Mamuda bisa zargin narka wa mijinta itace har ya mutu kan abinci a ƙaramar hukumar Fika a Yobe.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da kisan matarsa, Hauwa mai ɗauke da cikin wata 9 a Minna, babban birnin jihar Neja.
Wasu matan aure biyu sun gamu da kaddara mara kyau bayan sun kwankwaɗi maganin ƙara sha'awa domik yin gogayya da sabuwar amaryar mijinsu a Abuja.
Wani magidanci, Yahaya ya roƙi wata kotun yanki a Abuja ta raba aurensa da mai ɗakinsa, ya ce tun da ya musulunta zaman lafiya ya bar gidansa da matarsa.
An gurfanar da wani magidanci, Umar Inusa a gaban kotun shari'ar Musulunci a Kano bisa tuhumar raunata matarsa a ƙirji, alkali ya ɗage zaman zuwa watan Nuwamba.
Rikicin Ma'aurata
Samu kari