Rikicin addini
Rahotanni sun tabbatar da cewa an goge shafin Facebook na Fasto Ezekiel Dachomo yayin da ake cece-kuce kan kalamansa game da kisan Kiristoci a Najeriya.
Fasto Wilfred Anagbe ya bayyana a gaban Majalisar Dokokin Amurka, yana cewa Najeriya na fuskantar “kashe-kashe masu kama da kisan kare dangi” kan Kiristoci.
Shugaban CAN, Rabaran Daniel Okoh, ya ce suna maraba da shawarar Amurka ta taimaka wa Najeriya wajen kawo ƙarshen kashe-kashe da rashin tsaro a ƙasar.
Kungiyar Musulmai a jihar Edo sun kai gwamnatin jihar a kotu kan mika makarantun gwamnati ga cocin Katolika ba tare da tuntubar sauran bangarori ba.
Ana fargabar wasu Yahudawa sun kona wani masallaci a Yammacin Kogin Jordan, inda suka lalata gine-gine tare da rubuta kalaman batanci a bangon masallacin.
Gwamnatin Jamus ta haramta ƙungiyar Muslim Interaktiv, ta kuma yi samame a gidaje saboda zargin goyon bayan kafa tsarin Musulunci da ayyukan da suka sabawa doka.
Malamin addinin Kirista, Ladi Thompson ya soki gwamnatin tarayya, yana cewa akwai kisan kiyashi tun shekaru 20 da suka gabata saboda tsattsauran ra'ayi.
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya ba da umarnin rufe masallacin Juma'a a Donga bayan rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu da jikkata wasu.
Hadimin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga ya yi martani ga gwamnatin kasar Amurka kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya inda ya karyata jita-jitar.
Rikicin addini
Samu kari