Jam'iyyar PDP
Gwamnan Seyi Makinde ya aika da wasika ga majalisar jihar Oyo inda ya sanar da su kudurinsa na tafiya hutu tare da mika mulki ga mataimakinsa Bayo Lawal.
Jam'iyyar mai mulki a jihar Osun ta gamu da koma baya yayin da wasu mambobi sama da 100 suka jefar da laima, sun koma jam'iyyar APC ranar Lahadi, 21 ga wata.
Jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta yi babban kamu bayan daruruwan mambobin jam'iyyun adawa na PDP, APGA da LP sun dawo cikinta. Sun sha alwashin ba da gudunmawarsu.
Jam'iyyar PDP a jihar Edo ta bayyana fushinta kan komawar mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu zuwa jam'iyyar APC. Ta ce hakan ya nuna son kansa a fili.
Tsohon sakataren gudanarwa na kasa a PDP, Abubakar Mustapha da tsohon kwamishina a jihar Kaduna, Rabiu Bako duk sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin kwato jihar Edo daga hannun jam'iyyar PDP. Ya fara shirin cimma wannan kudirin.
Philip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya watsar da jam'iyyar PDP a jihar tare da komawa APC yayin da Abdullahi Ganduje ya karbe shi.
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya yi magana kan hadaka da jam'iyyun adawa domin kifar da gwamnatin Bola Tinubu inda ya gindaya sharuda.
Sanata Ali Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu ya yi martani kan bukatar ya sauya sheka zuwa PDP ko kuma wata jam'iyya kamar yadda aka sanar da shi.
Jam'iyyar PDP
Samu kari