Jihar Plateau
Wata 'yar jarida, ta bankado yadda wani likitan boge ke zubar wa 'yan mata ciki a unguwar Yan-Doya da ke Jos, jihar Plateau a kan N5,000 tare da jefasu a karuwanci.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar yin galaba kan 'yan ta'adda a jihohin Katsina da Plateau. Sojojin sun sheke dan ta'adda tare da ceto mutum biyu.
Podar Yiljwan Johnson wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa 'yan Najeriya za su sake yi zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Kungiyar raya al'adun karamar hukumar Bokkos a jihar Filato ta yi tit da kisan da wani soja ya yi a yankin yayin da yake bikin ƙarin shekara ranar Litinin.
Akalla 'yan bindiga bakwai ne suka ajiye makaman su tare da mika wuya ga gwamnatin jihar Filato bayan zaman sulhu. An ruwaito su ne ke addabar garuruwan Wase.
A yayin da jami'ar jihar Filato ta sanar da rufe makarantar na kwanaki 10, gwamnan jihar Mutfwang ya yi Allah-wadai kan harin da aka kai jami'ar da ke Bakkos.
Wasu gungun mata sun fantsama kan tituna suna zanga-zangar nuna adawa da yawan hare-hare da kashe-kashen ƴan bindiga a yankunansu a Bokkos da Mangu.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mahara sun kai hari mara daɗi kan al'umma a kauyen Butura da ke ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato, sun kashe rayuka uku.
Duk da wa'adin da aka sanya ya wuce, wasu maniyyata daga jihar Filato sun roƙi hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON ta taimaka ta karɓo cikon kuɗin na N1.9m.
Jihar Plateau
Samu kari