Jihar Plateau
Hukumar sojojin ƙasa ta ƙaddamar da sabon atisayen kakkaɓe ƴan bindiga a jihar Plateau. Shugaban hukumar, Manjo Janar Lagbaja shi ne ya ƙaddamar da atisayen.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya koka kan kwaranyowar 'yan ta'adda da wasu masu aikata miyagun laifuka zuwa jiharsa daga jihohin da ke makwabtaka da.
Rundunar sojoji a jihar Plateau ta ce ta kama shanu da awaki fiye da dubu daya da ke gararanba a gonakin mutane tare da yi musu barna a karamar hukumar Mangu.
Rundunar sojin Najeriya da ke karamar hukumar Mangu a jihar Plateau ta hallaka tsagera 'yan bindiga uku da kwato muggan makamai a hannunsu bayan wani artabu.
Dakarun sojoji na atisayen 'Operation Safe Haven' sun yi arangama da miyagun ƴan bindiga a jihar Plateau. Sojojin sun halaka ƴan bindiga uku da kwato makamai.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa a jihohin Plateau da Benue. Ya umarci jami'an tsaro da su cafko masu shirya su.
Dan Majalisar Wakilai daga jihar Filato, Dachung Musa Bagos, ya bayyana takaicinsa kan yadda ake samun karuwar hare-haren 'yan bindiga a jihar cikin kwanakin.
Ƴan bindiga sun sake kai hari a jihar Plateau inda suka halaka mutum tara da ƙona gidaje shida a yayin harin cikin ƙauyen Sabon Gari na ƙaramar hukumar Mangu.
Wata kotun yanki a jihar Plateau ta yanke wa wani yaro mai shekaru 18, Ibrahim Ali daurin watanni uku a gidan kaso ko kuma biyan tara N10,000 da diyya N20,000.
Jihar Plateau
Samu kari