Jihar Ondo
Dan takarar mataimakin gwamna na jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Ondo, Olayide Adelami, ya lashe zabe a rumfar zabensa. APC ta lallasa PDP a rumfar zaben.
Wani jagoran APC a jihar Ondo ya ce za su samu nasara a zaben gwamna da ake gabatarwa a jihar. Dan APC ya ce babu wata jam'iyyar adawa da za ta iya ja da APC.
Dan takarar jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP), Dr. Abass Mimiko, ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai tsoma baki ba a zaben gwamnan Ondo.
Jam'iyyar APC ta kakryata zargin PDP na cewa ta tura 'yan daba zuwa karamar hukumar Idanre domin hargitsa zaben gwamnan jihar Ondo. APC ta ce zancen kawai ne.
A yau ne ƴan takara 18 daga jam'iyyun siyasa daban daban za su kara a zaben gwamnan jihar Edo, Gwamna Lucky Aiyedatiwa na kokarin a zaɓe shi karon farko.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa da ke takarar gwamnan Ondo a jam'iyyar APC a zaben da ake yi ya ce zai karbi kaddara idan aka yi adalci ko da bai yi nasara ba.
Jam'iyyun siyasa sun ci kasuwar sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Ondo da ake yi yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024, an rika ba mutane takarda.
Rahotannin sun tabbatar da cewa yan daba sun yi ta harbe-harbe wanda ya tilasta mazauna wan yankin Ondo shigewa gidajensu saboda fargaba ana tsaka da zabe.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour (LP) a zaben Ondo Festus Ayo Olorunfemi ya kada kuri’a a zaben jihar da ke gudana. Bidiyo ya nuna lokacin da ya kada kuri'a.
Jihar Ondo
Samu kari