Labaran NNPC
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya magantu kan dambarwar da ke faruwa tsakanin kamfanin mai na NNPCL da kuma matatar man Aliko Dangote a Najeriya.
Majalisar wakilan kasar nan ta shawarci gwamnatin tarayya ta umarci NNPCL ya sahalewa yan kasuwa su fara sayo fetur kai tsaye daga matatar Dangote.
A rahoton nan, za ku ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi karin haske kan zargin batan Dala biliyan 49 daga asusun gwamnatin tarayya a zamaninsa.
Yayin da ake cigaba da rigima kan farashin man fetur tsakanin kamfanin NNPCL da matatar Aliko Dangote, Gwamnatin Tarayya ta fadi matsayarta kan haka.
Rabaran Gabriel Abegunrin ya ba gwamnatin tarayya shawara kan yadda fetur zai yi arha. malamin addinin ya bukaci a bar Dangote ya sayar da fetur ga 'yan kasuwa.
Kungiyar manyan ma'aikatan fetur da gas na kasa (PENGASSAN) ta ce za a samu matsala idan yan kasuwa su ka fara sayo fetur kai tsaye daga matatar Dangote.
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta IPMAN ta ce sun fara tattaunawa da matatar Ɗangote domin fara ciniki kai tsaye ba tare da biyowa ta hannun NNPCL ba.
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana yakinin cewa za ta iya fara sayen fetur kai tsaye daga matatar Dangote yayin da tsadar fetur ke kamari.
Tsohon shugaban NESG, Kyari Bukar ya bayyana cewa Bola Tinubu ya biyo hanya mai gargada wajen tuge tallafin man fetue shiyasa aka shiga ƙangin wahala.
Labaran NNPC
Samu kari