Labaran NNPC
Kungiyar PANEP mai rajin kare tattalin arzikin kasa ta yi zanga zangar goyon bayan matatar Dangote a jihar Kaduna. Kungiyar ta zargi PENGASSAN ta kulla makirci.
An samu takun saka mai zafi tsakanin Dangote da hukumomin gwamnati kan man fetur, samar da danyen mai, da rikicin ma’aikata a sabuwar matatar man Dangote.
Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), ya tabo batun illar da yajin aikin kungiyar manyan ma'aikatan man fetur na kasa (PENGASSAN) ya jawo a kasa.
Kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta kasa (PENGASSAN), ta tsudunma yajin aiki a fadin Najeriya. Lamarin ya kawo tsaiko a kamfanin NNPCL da NUPRC.
Matatar Dangote ta sanar da daina sayar da man fetur da Naira bayan korar wasu ma'aikata. PENGASSAN ta ce za ta yi bore domin adawa da korar ma'akatan.
NNPC ya samu N318.05bn daga Janairu zuwa Agusta, 2025 don nemo mai a yankunan Sokoto, Neja da wasu hudu, wanda ya zama 30% na ribar PSC daga rabon FAAC.
A labarin nan, za a ji cewa 'yan kasuwar mai sun harzuka bayan sun ji labarin cewa gwamnatin tarayya na shirin sayar da kadarorin hadin gwiwa da ta mallaka a NNPCL.
Kamfanin NNPC ya samu ₦1.06trn daga ribar PSC tsakanin Janairu–Agusta 2025 amma bai tura kudin rabosan ga FAAC ba, abin da ya jawo tambayoyi kan kudaden shiga.
Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa yan kasuwa da ke shigo da man fetur daga kasashen waje sun nemi ya saka musu tallafin man fetur na Naira tiriliyan 1.5.
Labaran NNPC
Samu kari