Matasan Najeriya
Jami'an tsaro sun farattaki matasa a kofar gidan gwamnatin Kano yayin da masu zanga zanga suka fara kona taya. Sun harba borkonon tsohuwa da harbi sama.
Rahotanni sun bayyana cewa daruruwan masu zanga-zanga sun haddasa cunkoson ababen hawa a hanyar Abuja zuwa Kaduna bayan toshe titi a Suleja da ke jihar Neja.
Jami'an ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar da suka matsa sai sun ga mai martaba sarkin Bauchi, sun harba masu barkonon tsohuwa mai sa hawaye.
Kungiyar lauyoyi ta kasa, NBA za ta ba masu zanga zanga da aka zalunta kariya kyauta a dukkan jihohin Najeriya. NBA ta yi umurni da saka ido a fadin Najeriya.
Gwamnan jihar Jigawa ya dauki hadimai kusan 200 a yayin da ake fama da wahalar rayuwa a Najeriya. Sakataren gwamnatin jihar, Bala Ibrahim ne ya sanar.
Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta tarwatsa wasu matasa da suka yi kokarin fasa wuraren adana kaya da wasu shagudan a' Zoo Road' da ke birnin Kano.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin kin sanar da wuraren siyar da shinkafa mai nauyin 50kg kan kudi N40,000 kacal inda ta ce ta yi hakan ne domin dalilai na tsaro.
Gwamnonin jihohi sun ja kunnen masu zanga zanga su bi hankali ban da yin duk wani abu da zai iya kawo tashin tashin a tsawon lokacin da za su ɗauka.
Mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara ya yi wakar martani bayan goge shafinsa na Facebook da talakawa suka nema a yi a kan wakar Bola Tinubu cikin sabuwar waka.
Matasan Najeriya
Samu kari