Matasan Najeriya
Zanga zanga ta ɗauki sabon salo a jihar Osun da ma wasu sassan Najeriya a rana ta biyar watau yau Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024 yayin da wasu suka fara cire kaya.
Bola Tinubu ya sha suka kan jawabin da ya gudanar a jiya Lahadi 4 ga watan Agustan 2024 inda suka ce bai yi magana kan bukatun masu zanga-zanga ba.
Gweamnatin Kano ta dauki matakai shida na ganin ta magance matsalolin masu zanga-zanga yayin da kuma ta yi magana kan daga turar Rasha da aka yi a jihar.
Ofishin jakadancin ƙasar Rasha a Najeriya ya nesanta gwamnatin ƙasar daga zargin hannu a ɗaga tutocinta da masu zanga zanga ke yi musamman a jihohin Arewa.
Tun fara zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya an samu muhimman abubuwa da suka ja hankalin al'umma wanda suka hada da daga tutar Rasha da jawabin Tinubu.
Matasa masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa sun toshe hanyoyi a jihhar Osun inda suka bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya biya musu bukatunsu.
Yayin da ake cigaba da zanga zanga a Najeriya, gwamnatin tarayya ta dage zaman majalisar zartarwa da ta saba yi duk ranar Litinin a fadar shugaban kasa.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan daba sun farmaki masu zanga-zanga da suka yi dafifi a kusa da ofishin Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas a ranar Litinin.
Solomom Dalung ya bayyana jawabin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ranar Lahadi a matsayin wanda ba ya kunshe da saƙon komai game da zanga zanga.
Matasan Najeriya
Samu kari