Matasan Najeriya
A labarin nan, za a ji cewa hukumar NDLEA reshen jihar Kano ta yi gam da katar da buhunan wiwi a wajen ceton wasu da hadarin mota ya rutsa da su a hanya.
A labarin nan, za a ji cewa hukumar Kwastam ta kasa ta bayyana cewa daruruwan mutane ne su ka nemi guraben aiki tun bayan sun tallata neman aiki a 2024.
An caccaki tsohon hadimin marigayi Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad bayan ya caccaki masu kiran yin zanga-zanga irin ta Nepal a Najeriya inda ya ce ba su da kunya.
Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a kasar Nepal, matasa sun ƙone gidan tsohon Firaminista, Jhalanath Khanal, inda matarsa Rabi Laxmi Chitrakar ta ke ciki.
Wani matashi ya yi tattaki daga Ikorodu zuwa Abakaliki na tsawon kwanaki 17 don godiya ga Gwamna Nwifuru, ya samu kyaututtuka ciki har da tallafin N10m.
Hukumar shige da fice ta Amurka ta kori 'yan Najeriya sama da 2,300 a cikin shekaru 11, inda aka sanya Najeriya a kan gaba a yawan 'yan Afirka da aka kora.
Hukumar DSS ta baiwa shafin sada zumunta X wa'adin awanni 24 don cire wani rubutu na Omoyele Sowore da ya yi kan zargin Bola Tinubu da makaryaci a Brazil.
Mutanen garin Bimasa a karamar hukumar Tureta ta jihar Sakkwato sun nuna jarumta da suka tunkari yan bindiga gaba da gaba, sun kashe yan ta'adda 10.
Shugaban kungiyar matasan APC, Arewa maso Gabas, Kabiru Garba Kobi ya ce sun 'yanta fursunoni 59, sun dauki nauyin karatun marayu 59, don taya Shettima murna.
Matasan Najeriya
Samu kari