Jami'o'in Najeriya
Ministan Kimiyya da Fasaha da ake zargi da amfani da takardun digiri da NYSC na bogi, Uche Nnaji ya shirya fitowa bainar jama'a domin kare kansa.
ASUU ta fara shirye-shiryen yajin aiki na kasa baki daya bayan gargaɗin kwanaki 14 ga gwamnati, tana zargin cewa ba a aiwatar da yarjejeniyar da 2025 ba.
Jami’ar Nsukka da ke jihar Enugu a Najeriya ta tabbatar cewa minista a gwamnatin Bola Tinubu bai kammala karatunsa ba kuma ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba.
Bayan jin cewa Rarara ya samu digirin girmamawa daga jami'ar European-American, Legit Hausa ta zakulo mawaƙan Hausa 5 da suka taɓa samun irin wannan karramawa.
Hukumar NUC ta yi gargadi ga dalibai yayin da ta fitar da sunayen jami’o’in bogi 58 da ke aiki ba bisa ka’ida ba a fadin Najeriya, suna ba da digiri marasa inganci.
A labarin nan, za a ji cewa Sanata Barau I Jibrin ya dauki nauyin karatun wasu dalibai 1000, kuma har sun fara karatu a jami'ar Dutsin Ma da ke Katsina.
Sadaukin Bauchi, Abdulrahman Sade, ya bayyana cewa zai yi bakin kokarinaa wajen ganin shahararren mawaki, Dauda Kahuti Rarara ya samu digirin girmamawa na gaskiya.
Jami’ar European-American ta yi martani kan maganganu da ake ta yi bayan rahoton karrama Dauda Kahutu Rarara inda ta ce ba ta da masaniya kan bikin da aka yi.
Mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya yi magana kan karrama shi da aka yi da digirin girmamawa da jami’ar European American ta yi a yau Asabar.
Jami'o'in Najeriya
Samu kari