Jami'o'in Najeriya
ASUU ta ce malamai na koyar da dalibai cikin yunwa da rashin kayan aiki, ta yi barazanar shiga yajin aiki saboda gwamnati ta gaza cika alkawuran da ta dauka.
ASUU, NASU, SSANU da NAAT sun tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani a LASU kan batun albashi da bukatar gwamnati ta aiwatar da karin albashi na kasa.
Asibitin koyarwa na jam'iar Maiduguri da ke Borno ya bude cibiyar fasahar ICT ta kiwon lafiya inda ta karrama Bola Tinubu ana rigimar sauya sunan UNIMAID.
Bayan Bola Tinubu ya sauya sunan jami'ar Maiduguri zuwa 'Muhammadu Buhari University', Kungiyar ASUU reshen UNIMAID za ta shiga kotu da gwamnatin tarayya.
A labarin nan, za a ji cewa majalisar dinkin duniya ta bayyana Farfesa Rabia Sa’id a matsayin daya daga cikin 'yan kwamitin duba illolin makamin nukiliya a duniya.
Daliban UNIMAID da masu ruwa da tsaki sun buƙaci Tinubu ya soke sauya sunan jami’ar, suna mai cewa UNIMAID ta fi suna, tana wakiltar juriya, ilimi da tarihin yankin.
Ana zargin Dr. Olabode Ibikunle ya rasu a otal yayin lalata da ɗaliba a Kogi, bayan ya sha maganin ƙara kuzari, kuma yanzu ’yan sanda na ci gaba da bincike.
Ma'aikatar ilimi a Najeriya ta yi magana game sauya sunan jami'ar Maiduguri saboda marigayi Muhammadu Buhari inda ta ce hakan abin a yabawa Bola Tinubu ne.
Shirin NELFUND da ke ba daliban Najeriya lamunin karatu ya shirya samar da shafi na musamman domin ba dalibai hanyoyin samun aiki a Najeriya da ketare.
Jami'o'in Najeriya
Samu kari