Jami'o'in Najeriya
Jami'ar Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ta bayyana alhininta bisa mutuwar ɗalibanta biyar a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su, ta dakatar da karatu.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shiga cikin batun takaddamar filin jami'ar BUK domin kawo karshen matsalar.
An bayyana yadda wasu tsagerun dalibai suka kutsa dakin kwanan dalibai tare da yiwa dalibai satar da ta dauki hankalin jami'an tsaro. AN kama wasu daga ciki.
Wata daliba a Jami’ar UNIZIK ta ciji malami bayan sun samu sabani kan daukar bidiyon TikTok. Jami’an tsaro sun fara bincike kan don gano gaskiyar lamarin.
Tinubu ya sauke shugabannin jami’o’i da dama, ciki har da Farfesa Aisha Maikudi ta jami’ar Abuja da Farfesa Chigbu na UNN, tare da nada sabbin shugabanni.
Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU), ta bayyana rashin jin dadin yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi shiru a kan bukatun da ta bijiro da su.
Majalisar dokokin Kano ta bayyana cewa ba za ta zuba idanu a rika kaskantar da rayukan dan adam ba a jihar, ganin yadda aka gudanar da rusau da tsakar dare.
shugaban kasa Bola Ahmed Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa jami'ar fasahar muhalli a yankin Ogoni a jihar Rivers bayan kafa wata jami'ar a Kudancin Kaduna
Shugaban jami'ar tarayya ta Gusau, Farfesa Muazu Abubakar, ya fito da bayanai a kan zargin cewa 'yan majalisa sun nemi shugabannin jami'o'i su bayar da cin hanci.
Jami'o'in Najeriya
Samu kari