Jami'o'in Najeriya
Gwamnatin tarayya ta sauya sunan Jami’ar Abuja zuwa Jami’ar Yakubu Gowon don girmama tsohon shugaban kasa. Kudurin yana jiran amincewar majalisar tarayya.
Ice Prince ya bayyana wahalhalunsa a matsayin maraya, ya gaza shiga jami’a saboda N20,000, amma ya ce nasararsa hujja ce cewa komai zai yiwu a rayuwa.
Jami'ar Sule Lamido ta amince da nazarin wakokin Nura M Inuwa. Mawakin ya bayyana wakokin da za a bincika, ciki har da "Hindu" da "Bakin Alkami."
Rahoto ya nuna cewa majalisar tarayya ta amince da kudurin da aka gabatar gabanta na kafa jami'ar ma'adanai ta tarayya a garin Jos, babban birnin jihar Filato.
Kungiyar ASUU reshen jami'ar LASU ta fara yajin aiki saboda rashin biyan karin albashi da gwamnati ta gaza aiwatarwa tun Janairu 2023. An ba dalibai hakuri.
Malamin jami'ar Uyo, Inih Ebong ya samu nasara a kotu bayan fafutkar shekaru 22 yana zuwa kotuna. Kotu ta umarci a biya shi hakkokinsa na shekarun.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana noma a matsayin hanyar kawo karshen yunwa, talauci da kuma rage shigo da abinci a kasar nan. Ya fadi alfanun jami'o'in noma.
Jami'ar jihar Taraba ta shiga jimami sakamakon rasuwar manyan malamanta har guda uku a tsakanin abin da bai wuce kwanaki uku ba, ma'aikata suɓ fara fargaba.
Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya sallami dukkan ƴan majalisar gudanarwa na manyan makarantun gaba da sakandire mallakin gwamnatin jihar Edo nan take.
Jami'o'in Najeriya
Samu kari