Jami'o'in Najeriya
Gwamnatin tarayya ta fara biyan ma'aikatan jami'o'i albashin da suke bi tare da biyan waɗanda suka yi ritaya hakkinsu, hakan na zuwa bayan NASU ta shiga yajin aiki.
Gwamnatin tarayya da gamayyar kungiyar ma'aikatan Najeriya sun gaza cimma matsaya domin kawo karshen yajin aikin da ake yi saboda hana su albashin wata 4.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya sallami shugaban jami'ar ABSU da ke garin Uturu tare da mataimakansa daga aiki, ya naɗa waɗanda za su maye gurbinsu.
Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) a jami'ar jihar Gombe ta janye yajin aikin da ta shiga. Ɗaliban jami'ar Gombe za su koma makaranta bayan yajin aiki.
Wani hazikin matashi, Ayodeji Akinsanya ya kammala karatun digiri a fannin lissafi da maki 4.97, ya kafa tarihi a jami'ar Ilorin da ke jihar Kwara.
Wata budurwa 'yar shekaru 19 ta kammala digiri, inda ta samu maki mafi girma a tsangayar da ta ke karatu, jama'a sun taya ta murna tare da mata fatan alheri.
Majalisar Dokoki ta gabatar da kudiri domin kirkirar Jami'ar Bola Tinubu wanda mataimakin shugaban Majalisar, Hon. Benjamin Kalu ya gabatar a gabanta.
Matar Bola Tinubu, Oluremi ta yi kyautar kudi N1bn ga jami'ar OAU yayin wata ziyara da ta kai. Oluremi Bola Tinubu ta bukaci a rika tsaftace muhallin jami'ar.
An fitar da jadawalin manyan jami'o'in duniya na 2025. An bayyana ABU, UI, da wasu 8 a matsayin manyan jami'o'in gwamnatin tarayya guda 10 mafi kyau a Najeriya.
Jami'o'in Najeriya
Samu kari