Labaran tattalin arzikin Najeriya
Gwamna Dikko Radda ya ƙaddamar da titin Ingawa–Dutsi–Shargalle mai tsawon 39km a Katsina domin bunƙasa kasuwanci da sauƙaƙa zirga-zirga a yankin.
Gwamnatin Tarayya ta amince da ayyukan N1.17tr a Kaduna, da suka haɗa da layin dogo mai tsawon 50km da hanyar Birnin Gwari domin haɓaka tsaro da tattalin arziki.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba z ata daina ciyo bashi ba matukar akwai bukatar hakan, ya ce karbo aron kudi ba aibu ba ne.
Majalisar dattawan Najerita ta bi sahun takwararta ta wakilai wajen amincewa da bukatar dauko aron Dala miliyan 516 domin gina titin Sokoto zuwa Badagry.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Najeriya karkashin kamfanin mai na NNPCL ta kara kudin danyen mai a kasuwar duniya saboda yakin Iran da Amurka.
Sanata Ireti Kingibe ta yi zargin cewa an canza wasu muhimman sassa na Dokar Zaɓe ta 2026 bayan majalisa ta gama aiki akai, musamman kan tsaron takardun ƙuri'a.
Wani jami'in matatar Dangote ya sanar da cewa ana saka tallafi a man fetur da dizil domin rage farashinsa a Najeriya. Sai dai ya ce hakan bai samu ba a man jirgi.
Masu ruwa da tsaki a harkar jiragen sama sun fara gargadi kan tashin farashin man jiragen sama a Najeriya. Ana fargabar hakan zai shafi farashin aikin Hajji.
Fadar shugaban kasa ta yi martani ga Sanusi II kan sukar Bola Tinubu d aya yi kan ciwo bashi duk da cire tallafin man fetur da aka yi a Najeriya.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari