Labaran tattalin arzikin Najeriya
Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa wasu daga kasashen waje na dakile cigaba a kasashen Afrika. Ya bukaci 'yan Afrika su tashi tsare a nahiyarsu.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya kaddamar da sababbin jiragen kasa masu tarago 24 a jihar Legas. 'Yan Arewa na korafi kan cewa an bar su a baya.
Hukumar IMF na shirin bai wa Najeriya da wasu ƙasashe tallafin $50bn domin rage raɗadin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haddasa. An gargadi Najeriya kan ciwo bashi.
Alkaluman DMO sun nuna cewa kudin da aka biyo Najeriya a matsayin bashi sun tabo Naira tiriliyan 159 zuwa karshen 2025, idan aka raba nana bin kowa N724000.
Cibiyar kididdiga ta kasa, NBS ta sanar da cewa farashin kayan abinci ya tashi da kashi 15.38 a watan Maris na 2026. Tashin farashin ya shafi Gombe, Zamfara, Taraba.
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ba za ta maido tallafin man fetur duk da tashin farashin man fetur a kasuwanni. Wale Edun ya ce za a tallafawa talaka.
Najeriya da Morocco za su sanya hannu kan yarjejeniyar gina bututun iskar gas na dala biliyan 25 a wannan shekara ta 2026. Aikin zai ratsa kasashe 13.
CBN ya fitar da sababbin dokokin BVN da za su fara aiki daga ranar 1 ga Mayu, 2026. Legit Hausa ta tataro abubuwa 5 da ya kamata ku sani gabanin wa'adin.
Manyan attajirai irin su Aliko Dangote da kamfanin NNPCL sun yi alkawarin bada Naira biliyan N30.5 domin tallafa wa shirin yaƙi da yunwa na Sanata Remi Tinubu yau.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari