Labaran tattalin arzikin Najeriya
Bankunan Najeriya 20 sun cika sharudan CBN na kara mallakar hannun jari zuwa Naira biliyan 500. UBA, Jaiz, Access, Taj Bank sun cika sharudan CBN.
Sanata Barau Jibrin ya kawo sabon shirin tallafawa jama'a a Kano ta Arewa. Zai raba kudi, motoci, babura, keken hawa, keken dinki, da tallafi a ilimi da kasuwanci.
Kasafin kudin Najeriya na 2026 na tiriliyan ₦58.18 na fuskantar barazana sakamakon faduwar farashin mai da matsalar samar da danyen mai a cikin gida Najeriya.
Kasafin kudin jihohin Najeriya na 2026 ya nuna yadda Lagos ta zarce Kano da ninki uku, tana mai dora hankali kan ci gaban hanyoyi, lafiya da ilimi.
Gwamnatin tarayya na shirin samun N5.4bn daga alhazan Najeriya ta hanyar kudin hidima na 2% don Hajjin 2026, IHR na neman bayyana hanyoyin amfani da kudin.
Faduwar farashin kayan abinci a Jihar Niger na jefa manoma cikin mawuyacin hali da gargaɗin tsaron abinci, koma baya na lalata harkar noma da gaza biyan basuka.
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ware Naira biliyan 2.3 a kasafin kudin shekarar 2026 domin biyan hakkoƙin tsofaffin shugabannin ƙasa da mataimakansu.
Shugaba Bola Tinubu ya yi hasashe cewa farashin kayan abinci zai sauka ƙasa da kashi 10 a 2026, yana nufin inganta rayuwa da bunƙasar tattalin arzikin Najeriya.
Bankin CBN ya fitar da hasashe game da yadda farashin man fetur zai kasance a Najeriya a 2026 lura da alkaluman tattalin arziki. Ya ce lita za ta kai N950 a 2026.
Labaran tattalin arzikin Najeriya
Samu kari